Falasdinu a ta bakin ministan harkokin waje Riyad al-Maliki ta caccaki kasashen da suka maido da huldar diflomasiyya da Israila a shekarar da ta gabata, a daidai lokacin da tashin hankali ke dada kamari tsakanin Falasdinawa da Yahudawa.
Al-Maliki ya shaida wa wani taron gaggawa na kungiyar kasashen Musulmai ta duniya cewa maido da huldar diflomasiyya da Isra’ila ba tare da samun kwanciyar hankalin da ake bukata ba na alamta goyon baya ga cin zalin da Yahudawa ke yi.
Kasashen da suka maido da huldar diflomasiyya da Isra’ila dai su ne: Sudan, Morocco, Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain.
A wani labarin na daban Isra’ila ta raba mutanen falasdinu dubu 10 da muhallansu inji majalisar dinkin duniya.
An dai shiga rana 6 a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa kan Falasdinawa a zirin Gaza, inda a yau asabar barin wutar jiragen yakin Isra’ilar ya kai ga kashe mutane 10 cikinsu har da kananan yara 8 a wani sansanin ‘yan gudun hijira.
Farmakin Isra’ilar ya kuma rusa gine-ginen da suka kunshi ofisoshin kamfanin dillancin labarai na AP da kuma kafar talabijin ta Aljazeerah.
Kawo yanzu akalla Falasdinawa 140 suka mutu cikin har da yara kanana 39, yayin da wasu kimanin 950 suka jikkata, tun bayan kaddamar da hare-haren da Isra’ila tayi kan birnin Gaza a ranar litinin da ta gabata.
A gabar yamma da kogin Jordan kuwa rahotanni sun ce jami’an tsaron Isra’ila sun kashe mutanen falasdinu akalla 13, yayin arrangamar da suka yi da Falasdinawan dake zanga-zanga kan neman dakatar da hare-haren da aka kaddamar kan birnin Gaza.
A bangaren Isra’ila kuwa, ta ce akalla mutane 9 mayakan Hamas suka kashe mata, sakamakon daruruwan rokokin da suka harbawa kan wasu biranen ta daga Gaza.
Majalisar dinkin duniya ta kiyasata cewar Falasdinawa dubu 10 sun rasa muhallansu dalilin rikicin da ya barke a makon jiya, tare da bayyana fargabar tagayyar da fararen hular suka yi ka iya fin haka muni a nan gaba kadan.