Falasdinu Ta Bukaci A Yi Waje Da Isra’ila A Kungiyar Tarayyar Africa.
Falasdinu ta bukaci kasashen Africa masu yanci su soke matsayin ‘yar sanya ido da aka baiwa Isra’ila a kungiyar tarayyar Africa ta AU.
Dama dai wasu kasashe mambobin kungiyar irinsu Africa da Kudu da Aljeriya duk sun kalubalanci matakin da aka baiwa mahukuntan yahudawan sahayoniyar a kungiyar.
Wata sanarwa da kungiyar Hamas, ta fitar ta ce matakin da aka baiwa Isra’ila ya keta dokokin kare hakkin dan adam da dabi’o’I na kungiyar ta AU, wanda ya tanadi yaki da wariyar launin fata da kuma kawo karshen duk wani salo na mulkin mallaka, da kuma mamayar wata kasa, kamar yadda yake faruwa ga falasdinu.
Hamas ta bukaci taron kolin na AU, dake gudana a birnin Adis Ababa, da ya dauki matakin yin waje da Isra’ila daga kungiyar.
Firaministan Falasdinu, Mohammad Shtayyeh, na halartar taron karo na 35 da sunan shugaban Falasdinawa Mahmood Abass.