Falastine: Isra’ilaTa Aiwatar Da Kame-Kame A Yankin Yamma Da Kogin Jordan
Labaran da suke fitowa daga yankin yamma da kogin Jordan wanda haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) take mamaye da shi, sun nuna cewa sojojin yahudawan sun aiwatar da kame-kame na matasa falasdinawa da dama.
Majiyar Falasdinawa a yankun ta bayyana cewa sojojin yahudawan sun kai farmaki kan falasdinawa da dama sun kuma shiga cikin gidajen wasu sun kuma kama matasa sun tafi da su wuraren bincike na musamman.
A garin Batkain dake yamma da garin Jenin yahudawan sun kama wani matashi a lokacinda yake wucewa ta shingen da suka sanya a kan titi a yankin.
Har’ila yau sun kama matasa guda biyu masu suna Qusai Amoor da Izzu Ziyad a wani kauye da ke kudu maso yammacin Jenin. Banda haka sojojin yahudawan sun kama Yusuf Faisal a lokacinda yake wucewa kusa da shingen da suka sanya a kusa da kauyen Humrah kusa da garin Toobass duk a yankin yamma da kogin Jordan.