Falasdinu; Amurka Na Rufa-rufa Akan Kisan Shireen Abu Akleh.
Hukumomin a Falasdunu, sun zargi gwamnatin Amurka da kokarin yin rufa rufa a kisan ‘yar jaridar nan ta tashar Al-Jazeera, Shireen Abu Akleh.
Wannan dai na zuwa ne bayan sanarwar da gwamnatin Washington ta bayar na cewa mai yiwuwa daga bangaren Isra’ila ne akayi harbin da ya kashe ‘yar jaridar a ranar 11 ga watan Mayun da ya gabata.
Kuma kwararun na Amurka da sukayi bincike kan harsashin da aka harbe ‘yar jaridar sun ce ba su da hujjar da take nuna cewa da gangan aka kashe ‘yar jaridar.
Mahukuntan falasdinawan sun danganta lamarin da yunkurin Amurka na neman boye gaskiyar abunda ya faru.
A shekaran jiya ne Falasdinu ta mikawa Amurka harsashin da aka hareb ‘yar jariodar domin gudanar da bincike kansa.
READ MORE : Burkina Faso; Mutane 34 Ne Suka Rasa Rayukansu A wasu hare-Haren Ta’addaci.
Kafin hakan dama Falasdinu da tashar ta Al-Jazeera mallakin gwamnatin Qatar, da ma wani bincike da kafofin yada labarai suka gudanar sun nuna cewa sojojin Isra’ila ne suka bindige ‘yar jaridar Shireen Abu Akleh, lokacin da take kan aiki a yankin Jenin lokacin wani samamen sojojin Isra’ila.
Saidai gwamnatin Isra’ila ta sa kafa ta shure duk wadanan zarge zargen.