Falasdinu; Akalla falasdinawa 2 Ne Suka Yi Shahada A Yankin Yamma Da Kogin Jordan.
Sojojin haramtacciyar kasar Isara’ila (HKI) sun kashe akalla Falasdinawa 2 a yankin yamma da kogin Jordan sannan wasu kimani 12 kuma suka ji raunuka sanadiyyar farmakin da sojojin yahudawan suka kai masu a garuruwan Jenin da kuma Nablos na yankin yamma da kogin Jordan a yau Lahadi.
Kamfanin dillancin labaran Ma’an ta Falasdinawa a yankin ta bayyana cewa Abu-Subh dan shekara 29 da kuma Muhammad Al-Azizi dan shekara 22 a duniya sun yi shahada a asbitin Rafadia dake Nablus a safiyar yau Lahadi sanadiyyar harbi da harsasai wanda sojojin yahudawan suka yi masu
Labarin ya kara da cewa wasu faladinawa 19 ne suke jinya a asabitin bayan fafatawan da suka yi da sojojin yahudawan wadanda suka shigo wadannan wurare.
Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan sun tura wasu sojojin dauki da bindigogin da ake cillawa daga nesa daga kuma kan gine-gine don kashe daddaikun mutane a garin na Nablus da kuma unguwar Ras al-Ain na garin Nablus.
Sai dai duk tare da makaman da suke da su falasdinawan sun tilastwa sojojin mamaya janyewa daga wadannan yankuna. Yahudawan Isra’ila kimani 600,000 suke zuwana a yankuna 230 a yankin yamma da kogin Jordan tun bayan yakin shekara ta 1967.