Falasdinawa Suna Da Karfin Harba Makamai Masu Linzami 150 Cikin Mintuna Biyar.
Shugaban bangaren siyasar kungiyar Hamas ta Falasdinu ya bayyana cewa: Suna da karfin harba makamai masu linzami 150 cikin kasa da mintuna 5 da za su yi raga-raga da Haramtacciyar kasar Isra’il.
A jawabin da ya gabatar a zaman taron kungiyar Hamas a garin Saida na kasar Lerbanon: Shugaban bangaren siyasar kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta Falasdinu Isma’il Haniyya ya jaddada cewa: Al’ummar Falasdinu a yanzu tana rayuwa ce a wani lokaci da take samun gagarumin sauye-sauye a fagen dabarun yaki da hasashen nasara, kuma duk da killace yankin Ziri Gaza amma ‘yan gwagwarmaya suna cikin shirin tunkarar duk wani makircin yaki da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isrea’ila za ta kaddamar.
READ MORE : Ayatullah Khamenei; Hajji aiki ne na siyasa.
Haniyya ya jinjinawa al’ummar Lebanon yadda ta rungumi Falasdinawa a matsayin ‘yan uwa kuma Lebanon Larabawa ne masu dauke da ruhin gwagwarmaya da nuna jin kai ga Falasdinawa tsawon shekaru 74 da suka gabata.
READ MORE : Wakilan Yankin Hong Kong Na Kasar Sin Sun Bayyana Halin Da Ake Ciki A Yankin A Wajen Taron UNHRC.
READ MORE : Legas – An Kama Wani Mutum Da Kullin Hodar Ibilis A Al’aurarsa.