Rikicin dake gudana tsakanin kasar Isra’ila da Falasdin ya tilastawa kamfanonin jiragen sama dakatad da zuwa kasar Yahudawan yayinda ake kira ga kasashen duniya su sanya baki.
A cewar AFP, Kawo ranar Alhamis, akalla kamfanonin jiragen kasashe bakwai sun sanar da cewa jiragensu zasu daina zuwa Izra’ila sakamakon Rikicin .
Ga jerinsu:
1. KLM Kamfanin KLM na kasar Holland ya dakatad da zuwa Isra’ila bayan fara Rikicin , a yanzu, tashar NOS ta bayyana.
2. BA, Virgiin Kamfanin kasar Birtaniya ya dakatad da dukkan jiragen da suka shirya zuwa Tel Aviv ranar Alhamis, hakazalika kamfanin Virgiin Atlantic ranar Alhamis a Juma’a.
3. Lufthansa Kamfanin Lufthansa na kasar Jamus ya sanar da cewa “muna sa ran komawa tashi zuwa Isra’ila ranar Asabar, 15 ga Mayu.”
4. Aeroflot
5. Iberia Kamfanin jirgin na kasar Spain ya fasa tafiyar da yayi niyya zuwa Isra’ila na ranar Alhamis da kuma Asabar.
Wata mai magana da yawin Iberia ta bayyanawa AFP cewa ” Zamu yanke shawara kan yadda abubuwa zasu kasance dangane da yadda abubuwa suka kasance.”
6. Kamfanin jirgin US Kamfanonin jiragen AMurka akalla 3; United, Delta da American Air sun dakatad da jiragensu daga zuwa Isra’ila.
7. LOT Kamfanin jirgin na kasar Poland ya “dakatad da zuwa Isra’ila a yanzu”. Kakakin kamfanin Krzysztof Moczulski ya ce: “Ina tunanin ba zamu je na da wasu kwanaki ba.”
Rikicin tsakanin falasdinawa da yahudawa dai ya barke ne sakamakon hare haren rashin imani da yahudawan suka fara kaddamarwa a kan musulmi falasdinawa inda daga baya suma falasdinawan suka fara maida martani.
An tabbatar da cewa rikicinn yana neman ya fi karfin gwamnatin izra’ila wacce yahudawa ke gudanarwa, domin basuyi zaton falasdinawan zasu iya samun karfin kare kai daga zaluncin da yahudawan suka jima suna aiwatarwa ba.
Bayan soma Rikicin dai an ta samun goyon bayan falasdinawan daga sassan duniya inda ake Allah wadarai da zaluncion yahudawa a kan raunanan falasdinawan.
READ MORE;Gwamnatin Buhari Tayi Batan Basira, Inji Gwamnan Jihar Bauchi
Abin takaici mayan kasashen larabawa masu ikirarin musulunci irin su saudiyya sunyi shiru bisa wannan rikici, amma kasashe irin su Iran,Turkiyya,Iraqi,Siriya da kuma yemen da sauran su sunyi magana dangane da matsalar dake faruwa a kan falasdinawan.