Wakilin kafar sadarwa na Al-Jazeera ne ya rawaito cewa, gomomin falasdinawa dake kan layin karbar tallafin abinci ne sojojin Isra’ila suka harbe, wadanda kuma a take suka ra sa rayukan su yayin da wasu kuma da dama suka ji raunuka.
Hare haren jiragen yakin Isra’ila a sansanonin Nuseirat, Bureij da Khan Younis duk a yankin na Gaza sun kashe a kalla mutane 30.
Kungiyar Save The Children ta bayyana cewa, duniya tana shaida yadda ake kashe kananan yara cikin kwanciyar hankali a Gaza.
Ma’aikatar lafiya ta Gaza ma ta bayyana cewa, yara shida ne suka rasa rayukan su a arewacin Gaza sakamakon rashin ruwa da abinci mai gina jiki yayin da wasu da dama ke cikin mawuyacin hali.
A wani labarin na daban New Zealand ta kakaba takunkuman Tafiye Tafiye Kan Isra’iliyawa Masu Tsatstsauran Ra’ayi
Kamar yadda kafar sadarwa ta Al-Jazeera ta rawaito, sanarwa ta fito daga ofishin firayi ministan New Zealand Christopher Luxon da kuma minstan harkokin waje Winston Peters inda take tabbatar da kakaba takunkuman tafiye tafiyen a kan wasu yahudawan Isra’ila wadanda aka san su da tsatstsauran ra’ayi.
Luxon yace, New Zealand ta damu matuka kan tashe tashen hankula da ‘yan Isra’ila keyi a kan falasdinawa a cikin wadannan watannin.
Peters kuma ya bayyana kokarin New Zealand na cigaba da gina matsugunai matsayin abin damuwa.
Hakan na zuwa ne a dai dai lokacin da ministan kudin Isra’ila Bezalel Smotrich yake sanar da shirin gina sabbin gidaje 3300 a gabar yammacin kogin Jordan da Isra’ilan ta mamaye.
Duba Nan: Babu Amintaccen Waje A Gaza
Sai dai kuma sanarwar ta kakaba takunkuman da New Zealand zatayi bata fayyace mutanen da za’a sanyawa takunkuman ba amma dai ta tabbatar da cewa masu tsatstsauran ra’ayi daga cikin mutanen da suke daga Isra’ila ne takunkuman za su shafa.