Faisal Bin Farhan Ya Ce Saudiya Na Jiran Zagaye Na 5 Na Tattaunawa Da Iran.
Ministan harkokin wajen kasar Saudiya ya bayyana cewa kasarsa tana jirin zagaye na 5, na tattaunawa tsakaninta da Iran.
Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran ta nakalto Faisal Bin Farhan yana fadar haka a taron tsaro da ke gudana a halin yanzu a birnin Munikh na kasar Jamus. Ya kuma kara da cewa an gudanar da zagaye na tattaunawa na 4 kuma na karshe, a ranar 21 ga watan Satumban shekara ta 2021 a birnin Bagdaza na kasar Iraki.
Bin Farhan ya kara da cewa gwamnatin kasar Saudia zata ci gaba da goyon bayan gwamnatin AbduRabbu Mansur Hadi a kasar Yemen, duk da cewa suna neman hanyoyin tsagaiya budewa juna wuta a gwamnatin San’aa.
Iran dai ta sha nanata cewa a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da kasar Saudiya kan dukkan matsalolin da ke tsakanin don warwaresu. Amma gwamnatin Saudiya bata dauki matakan da suka dace na ci gaba da tattaunawar ba.
Har’ila yau Bin Farhan ya gana da tokwaransa na kasar Amurka Antony Blinken a gefen taron na Munick inda suka tattauna batun shirin Nukliyar kasar Iran da kuma tattaunawar da ke gudana a birnin Vienna dangane da shirin.