Fafaroma Francis kuma shugaban mabiya Darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis ya gana da babban Hafson sojin kasar Myanmar, a ziyarar da ya fara yau zuwa kasar mai rinjayen mabiya addinin Budda, wadda kuma yanzu haka ke ci gaba da fuskantar suka daga kasashen duniya kan cin zarafi da kisan gillar da su ke yiwa tsirarun Musulmi ‘yan kabilar Rohingya da ke kasar.
Da safiyar yau ne dai daruruwan yara daga kabilu daban daban sanye da kayan gargajiya rike da furanni suka tarbi shugaban na Mabiya addinin Kirista Fafaroma Francis a filin jirgin saman Myanmar da ke Yangon babban birnin kasar baya ga manyan jami’an gwamnatin kasar da suka karbe shi a hukumance.
Bayan Isowar Fafaroman ne kuma ya yi wata ganawa ta musamman da babban Hafson sojin kasar, Janar Min Aung Hlaing a masaukinsa da ke birnin na Yangon, inda suka tattauna kan batutuwan da suka shafi tsaro dama zargin da ake kan jami’an sojin kasar na muzgunawa musulmi ‘yan kabilar Rohingya.
A gobe Talata ne kuma ake saran Fafaroman zai yi wata ganawa ta musamman da shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi wadda kima da martabarta ke kara zubewa a idon duniya bayan da ta gaza tabuka abin kirki kan kisan da ake yiwa Musulmi ‘yan kabilar Rohingya.
Manufar ziyarar ta kwananaki hudu da Fafaroma Francis ke gudanarwa ita ce jan hankali ga mabanbantan addinai da kabilun da ke kasar ta Myanmar don samar da zaman lafiya.
Fafaroma Francis ya gudanar da sujada ta musamman don tunawa kasar Myanmar a Lahadin nan, inda ya jaddada kiraye-kirayen da yake na kawo karshen tashin hankali a kasar da ake ta zub da jini tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.
Sujadar Mass din da aka gudanar a majami’ar Saint Peter Basilica ta birnin Vatican na zuwa ne bayan kiraye kirayen zaman lafiya da shi Fafaroma Francis, wanda ya ziyarci Myanmar a watan Nuwamban 2017 ya shafe watanni yana yi.
Wata limamiyar ‘yar asaklin Myanmar ce ta gabatar da karatun farko cikin harshen Burma a sujadar da ta samu halartar limamai mata da maza kimanin 200.
A wani alabarin na daban shugaban Mabiya darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis, ya fara ziyarar Thailand da zuwa wani wurin ibadar Budha domin ganawa da shugaban su.
Cikin ayyukan da Fafaroman zai yi sun hada da ganawa da shugaban kasa da Firaminista da kuma gudanar da addu’oi a bainar jama’a wadda ake saran dubban mutane su halarta
Francis ya gana da shugaban addinin Budha a yau Alhamis a wani wurin bautarsu dake birnin Bangkok a ziyarsa ta nahiyar Asiya don habaka dangantaka tsakanin addinai.
Wannan ce ziyarar shugaban darikar Katolikan ta farko a kasar Thailand wacce mabiya addinin Budha ne suka fi rinjaye, daga nan ne kuma zai garzaya Japan a ranar Asabar,bayn ya jagoranci sujadar dubban mabiya Katoloika a fadin kudu maso gabashin Asiya.