EU, Ta Nanata Goyan Baya Ga Yarjejeniyar Nukiliyar Iran.
Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta sake nanata goyon bayan ta ga yarjejeniyar nukiliyar Iran, a daidai lokacin da ake taron gwamnonin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya.
Sanarwar da EU, ta fitar ta ce Kungiyar ta kuduri aniyar yin aiki tare da kasashen duniya wajen kiyaye wannan yarjejeniya, wadda ke da matukar muhimmanci.
Wannan dai na zuwa ne bayan da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukliya ta duniya IAEA ya fitar da wani rahoto da Iran ta danganta da na bangaranci, wanda IAEA, ta ce bata samun cikaken goyan baya daga Iran.
READ MORE : Isra’ila Ce Silan Duk Wani Rikici A Gabas Ta Tsakiya Inji MDD.
A wata hira da ya yi da babban jami’in harkokin wajen Tarayyar Turai Josep Borrell a ranar Juma’ar da ta gabata, ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian ya yi gargadin cewa duk wani mataki na siyasa da hukumar ta IAEA za ta dauka, za a samu mai da martani daidai gwargwado nan take.
READ MORE : MJTF Ta Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Da Dari Takwas A Tafkin Chadi.
READ MORE : Iran Za Ta Iya Sauya Matsayarta Dangane da Hadin Kan da Take Baiwa IAEA.