Kungiyar Tarayyar Turai EU ta sanya sunayen ‘ya’yan shugaban kasar Rasha Vladimir Putin mata biyu da wasu mutane sama da 200 cikin bakin kundi, a wani bangare na sabon takunkumin da ta laftawa kasar Rashan sakamakon mamaye Ukraine da take cigaba da yi.
A jumlace dai kimanin ‘yan Rasha da masu alaka da su 217, kungiyar EU ta sanya sunayensu cikin bakin kundinta.
Dangane da ‘ya’yan shugaba Putin kuwa, da suka hada da Maria Vorontsova da Katerina Tikhonova, tuni dama Amurka da Birtaniya suka sanya musu takunkumi.
Mahaifiyar yaran ita ce tsohuwar matar shugaban Rasha Lyudmila, wadda aka sanar ta rabu da Putin a cikin shekarar 2013.
A wani labarin na daban An dakatar da fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hollywood Will Smith daga halartar bukukuwan gasar Oscar na tsawon shekaru 10.
Shugabannin gasar karrama jaruman fina-finan ta Oscar kusan dubu 10 ne suka yi taro da safiyar jiya Juma’a don tattaunawa kan marin da Will Smith ya shararawa jarumin barkwanci Chris Rock.
Sai dai hukuncin na su bai soke kyautar gwarzon gasar ta Oscar da Smith ya samu a watan da ya gabata ba, saboda fim din da ya kasance tauraro a cikinsa wato “King Richard”.
Zalika ba a hana Will Smith tsayawa takarar gasar ta Oscar a nan gaba ba.
A cikin taƙaitaccen bayani kan hukuncin da ya hau kansa, Smith ya bayyana amincewa tare da mutunta matakin da aka dauka a kansa.