Kungiyar tarayyar Turai EU ta bada sanarwan cewa ta karbi martanin Jumhuriyar Musulunci ta Iran dangane da shawarwarin da suka bayar saboda farfado da yarjeniyar JCPOA ta shirin Nukliyar kasar Iran.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Nabila Massra’il kakakin Josept Borrel jami’il mai kula da al-amuran kasashen waje na tarayyar ta Turai tana fadar haka a yau Talata a birnin Vienna na kasar Austria.
Massra’il ta kara da cewa kungiyar tana nazarin martanin sannan tana tuntubar kasashen Turai wadanda abin ya shafa da kuma gwamnatin Amurka dangane da shi.
A jiya Litinin ta yamma ce gwamnatin kasar Irann ta bada sanarwan cewa ta mika martaninta ga shawarorin da kungiyar ta EU ta gabatar don farfado da yarjiniyar JCPOA. Sannan ta kara jaddada cewa a halin yanzu ya ragewa gwamnatin kasar Amurka ta nuna cewa da gaske take kan farfado da yarjejeniyar da kuma dagewa kasar Iran takunkuman da ta dora mata, sannan ta dawo cikin yarjeniyar.
A wani labarin na daban Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya zargi gwamnatin kasar Amurka da kokarin tsawaita yakin Ukrain da kuma rikita yankin Asia da Pacific tare da ziyarar da Nancy Pelosi ta kai tsibirin Taiwan.
Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto Putin yana fadar haka a yau Talata a taron kasa da kasa na tsaro wanda aka bude a yau a birnin Mosco.
Ya kuma kara da cewa makaman da kasashen Turai da Amurka suke turawa zuwa Ukraine da kuma takunkuman tattalin arzikin da suka dorawa Rasha yana nufin basa son ganin bayan wannan yakin nan kusa.
A cikin watan fabrairun da ya gabata ne gwamnatin kasar Rasha ta fara yaki a kasar Ukraine saboda rashin amincewar gwamnatin Ukraine, ballewar yankunan Danesk da Luhang a matsayin yentattun kasashe.
Putin ya kammala da cewa ziyarar kakakin majalisar wakilan kasar Amurka Nancy Pelosi zuwa tsibirin Taiwan na kasar Cana, da ganging aka yi shi don ingiza kasar Rasha ta fada tarkon su.
Source: ABNA