EU Ranar Talata Ake Komawa Bakin Tattaunawar Vienna.
Kungiyar tarayyar turai ta EU, ta sanar da cewa a gobe Talata ne ake komawa bakin tattaunawar Vienna, da aka soma da nufin farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran.
Iran ma a nata bangare ta tabbatar da batun, inda ta ce tawagar kasar za ta kama hanyar zuwa birnin na Vienna yau domin halartar tattaunawar.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Saeed Khatibzadeh, yayin yayin taron manema labarai na mako-mako a yau Litinin, ya bayyana cewa, Iran na fatan dukkan bangarorin da batun yarjejeniyar ya shafa su sauke nauyin da ke wuyansu.
Ya kuma bayyana fatan ganin an cimma yarjejeniya a Vienna.
Tattaunawar ta wannan karo ta zo ne ‘yan kwanaki kadan bayan da Amurka ta sanar da janye wa Iran wasu takunkumai da suka shafi shirinta na nukiliya na zaman lafiya, matakin da Iran ta yaba saidai ta ce bai wadatar ba, don kuwa tana bukatar a dage mata takunkumi da ya shafi harkokin tattalin arzikinta da ya tagayara sakamakon takunkuman da tsohuwar gwamnatin Amurka ta kakaba mata, bayan da tsohon shugaban kasar Donald Trump, ya yi gaban kasan ya janye kasarsa daga yarjejeniyar ta 2015.