Enrique Mora Ya Ce Zai Ziyarci Iran Game Da Tattaunawar Vienna.
Mukadashin babban jami’in harkokin waje na kungiyar tarayyar turai Enrique Mora y ace zai ziyarci birnin Tehran inda zai gana da babban mai shiga tsakani na Iran a tattaunawar Vienna Ali Bagheri Kani.
Ziyarar na da manufar tattauna batutuwan da suka rage masu tsarkakakiya game da tattaunawar Vienna da ta shiga halin rashin tabbas.
Mista Mora, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin hadin gwiwa na yarjejeniyar nukiliya, zai zo ne Tehran domin tattaunawa da manyan jami’an kasar kan muhimman batutuwan da suka shafi farfado da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da Iran a 2015.
Tattaunawar Vienna da aka kwashe tsawon lokaci ana yi ta shiga halin rashin tabass ne tun bayan da Amurka ta ce ba za ta janye takunkumin da ta kakabawa dakarun kare juyin juya halin musulinci na Iran ba, wanda kuma daya ne daga cikin sharuddan da gwamnatin Tehran ta gindaya domin cimma yarjejniya.
A wani labarin kuma shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, Rafael Grossi, ya bayyana gaban wani kwamitin kungiyar tarayyar turai cewa, ya damu matuka game da halin da ake ciki a Iran, inda ya yi zargin cewa a cikin ‘yan watannin nan sun gano wasu alamu na tace uranium a wasu cibiyoyin nukiliya da Iran bata taba bayyanawa ba, saidai kawo yanzu Iran din bata maida martani kan kalamman nasa ba.