Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana nadin sabbin ministocin harakokin waje da na tsaro a yau Juma’a, awani bangare na garambawul da ya kudiri aniyar yi wa majalisar zartarwar gabanin zaben ‘yan majalisar dokoki kasar a wata mai kamawa.
Sebastien Lecornu, tsohon ministan harkokin yankunan Faransa na kasashen waje, ya samu ci gaba zuwa matsayin ministan tsaro, kamar yadda shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Faransa Alexis ya sanar a fadar ta Elysees.
Emmanuel Macron zai aiwatar da manufofin gwanatinsa
Sakamakon farko da aka gabatar ya nuna cewar Emmanual Macron ya samu tsakanin kashi 57.0 zuwa kashi 58.5 na kuri’un da aka kada, yain da abokiyar takarar sa Marine Le Pen mai ra’ayin rikau ta samu tsakanin kashi 41.5 zuwa kashi 43.0 na kuri’un.
Sakamakon zaben ya nuna raguwar banbancin tazara tsakanin yan takarar biyu kamar yadda aka gani a shekarar 2017 lokacin da suka fafata a tsakanin su a zagaye na biyu.
Amma duk da haka wannan nasara zata baiwa Macron damar ci gaba da jagorancin gwamnati da kuma aiwatar da manufofin sa na Karin shekaru 5 masu zuwa.
Macron ya zama shugaban Faransa na farko da ya samu nasarar yin wa’adi na biyu tun bayan shugaba Jacques Chirac a shekarar 2002, yayin da shugaba Nicolas Sarkozy da Francois Hollande suka yi wa’adi guda guda.