Fitaccen biloniyan duniya, Elon Musk, ya fasa siyan kamfanin sada zumuntar zamani na Twitter wanda aka fara ciniki da shi Musk ya bayyana cewa, ya fasa ne saboda kamfanin sun ki bashi tarin bayanai kan asusun bogi, wanda ginshiki ne na kasuwanci.
Sai dai kamfanin Twitter sun matukar fusata saboda sun bai wa Musk damar ratsa “firehouse”, kundin bayanai da daruruwan miliyoyin wallafa na tsawon wata daya.
Elon Musk, fitaccen biloniyan duniya kuma mamallakin Tesla Inc., yace ya janye daga cinikin kamfanin Twitter da yake yi kan kudi $44 biliyan inda ya kara da cewa kamfanin kafar sadarwan ta gaza bashi bayanai kan asusun bogi a kafar.
Musk ya sanar da hakan ne a r anar Juma’a kamar yadda Reuters ta ruwaito.
Wannan cigaban ya zo ne bayan da Twitter ta bai wa Musk damar duba “firehouse” dinta, wani kundin bayanai kan daruruwan miliyoyin wallafa na kowacce rana a watan da ya gabata.
A wani bayani, lauyan Musk yace Twitter ta gaza ko kuma ta ki yin martani kan bukatun bayar da bayani kan susun bogi a kafar, wanda ginshiki ne na kasuwancin kamfanin.
A kokarin mayar da kamfanin sada zumuntar mai zaman kansa, biloniyan ya ce zai siya Twitter kan kudi har $43 biliyan a watan Afirilun da ya gabata.
Daga bisani ya yarje kan cewa zai siya kamfanin a $44 biliyan. Amma bayan an gama kai ruwa ana, Musk ya yanke shawarar fasa siyan kamfanin inda ya dogara da dalilan asusun bogi a kafar.
Hamshakin mai arzikin duniya, Elon Musk ya taya Twitter kan $43bn, zai siye ta baki daya A baya dai, Legit.ng ta rahoto muku cewa, mutumin da ya fi kowa kudi a duniya, Elon Musk yana son siyan Twitter don ya maida shi mallakinsa, mujallar Bloomberg ta ruwaito.
Kamfanin Twitter ta sanar a ranar Alhamis cewa, Elon Musk, wanda yafi kowa hannun jari a Kamfanin, ya bukaci a siyar masa da sauran hannayen jarin manhajar kafar sada zumuntar zamanin a kan $54.20 ga duk hannun jari, wanda gaba daya darajarsa tafi $43 biliyan.
Daily Trust ta ruwaito cewa, a cewar Musk, wannan farashin shine iya abunda zai iya siya, idan kuma basu amince da hakan ba, zai sake tunani a kan matsayinsa na mai hannun jari.