ECOWAS Ta Nada Mahamadu Issufu Wakilinta Kan Rikicin Burkina Faso.
Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS sun yanke shawarar wakilta tsohon shugaban kasar Nijar Mahamadu Isufu a matsayin mai shiga tsakani kan rikicin Burkina Faso, inda sojoji suka kifar da mulkin tsohon shugaba Rock Marc Kabore.
A cikin sanarwar bayan taronsu shugabannin kasashen na Ecowas, sun ce lura da kokarin da Burkina Faso ta yi ta fuskar tsaro, da dawo da ‘yan gudun hijira yankunansu duk da kalubalen da ta ke fuskanta.
Ta fuskar jin kai, lura da halin da ake ciki Ecowas tayi kira ga kasashen duniya da su karfafa taimakon jin kai a Burkina Faso.
Taron ya kuma yaba da yadda sojojin suka bar tsohon shugaba Kaboré ya koma gidansa tare da jaddada bukatar neman a bas hi ‘yanci baki daya.
READ MORE : Iran Ta Jajantawa Bangaladesh Kan Iftila’in Gobarar Data Kashe Mutum 49.
Ecowas ta kuma bukaci sojojin dake mulki a kasar ta Burkina faso dasu gaggauta dawo da tsarin mulki cikin gajeren lokaci.
READ MORE : Yamen; Rayukan Yara 3,182 Suka Salwanta A Cikin Shekaru Takwas.
READ MORE : Kasashen Musulmi Na Tir Da Kalaman Batancin Da Akayi Wa Annabi Muhammad (saw) A
READ MORE : Nijar; Za A Yi Wa ‘Yan Ta’adda Afuwa Idan Suka Ajiye Makamasu Suka Rungumi Zaman lafiya.