Shugabannin kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) sun kakaba wa jagororin juyin mulkin Guinea takunkumi, kana suka bukaci a gudanar da zabe nan da watanni 6 don maido da mulkin demokaradiyya cikin hanzari a kasar, bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin Alpha Conde a farkon wannan wata.
Ta yi kira ga kungiyar Tarayyar Afirka da ta Tarayyar Turai da su goyi bayan takunkuman da da ta kakaba wa gungun sojojin da suka yi juyin mulkin, wadanda suka kira kansu da kwamitin sansantawa da kawo ci gaba.
Kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO mai mambobi 15 ta riga ta dakatar da Guinea sakamakon juyin mulkin na ranar 5 ga watan Satumba da jagoran dakaru na musamman a kasar Kanar Mamady Doumbouya ya yi.
Wannan juyin mulki da sojoji suka yi a kasar Guinea ya janyo damuwa a tsakanin kasashen duniya ganin yadda demokaradiyya ke gamuwa da koma baya a yammacin Afirka, duba da yadda Mali ta gamu da juyin mulki har 2 tun a watan Agustan bara.
Sai dai a jawabinsa ga masu su ruwa da tsaki a siyasar kasar, jagoran juyin mulkin Guinea, Kanar Mamady Dombouya, ya jaddada cewa gazawar ilahirin ‘yan siyasan kasar ce ta tilasta masa kifar da gwamnatin farar hula.