Shugabannin kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ke taro a Accra babban birnin kasar Ghana, domin tattaunawa kan yadda za su warware rikicin siyasar kasar, da sojoji suka yi juyin mulki sau 2 cikin watanni 9.
Daga cikin shugabannin dake halartar taron na yau dai akwai shugaban sojojin da suka yi juyin mulkin na Mali Kanal Assimi Goita, shugaban Ivory Coast alassane Ouattara, shugaban Najeriya Muhd Buhari da kuma Christian Marc Kabore na Burkina Faso.
Kafin taron na yau Lahadi dai, kungiyar at ECOWAS tayi barazanar kakabawa gwamnatin sojojin ta Mali takunkumi, bisa abinda ta kira jefa makomar kasar cikin hatsari da suka yi.
A ranar litinin da ta gabata, Kanal Assimi Goita da ya jagoranci yiwa tsohon shugaba Ibrahim Boubacar Kieta juyin Mulki, ya sake kwace mulkin bayan tsare shugaban rikon kwarya na farar hula Bah Ndaw da Firaministansa Moctar Ouane wadanda aka saki a ranar Alhamis bayan da suka yi Murabus.
Kanal Goita ya jagoranci juyin mulkin farko ne a watan Agustan 2020 bayan da tsohon shugaba Keita ya fuskanci zanga-zangar gama gari ta neman yayi murabus saboda gazawarsa wajen magance matsalolin tsaro da na tattalin arziki.
Amma mutanen najeriya sun koka yadda shugaban nasu muhammadu buhari ya tsallake tulin matsalolin da ake fuskanta da suka hada da na tsaro da ttalin arziki ya tafi taron na kungiyar kasashen yammacin afrika (ECOWAS).
Shugaba muhammadu buhari na anjeriya dai ya bar kasar sa najeriya a yammacin wannan rana domin halartar taron kungiyar kasashen yammacin afrika (ECOWAS) din wanda hakan ke nuna kamar bai damu da mawuyacin halin da ake ciki a najeriya din ba.
An zura idanu domin a ga yadda taron zai kaya, kamar yadda aka tabbatar taron na shugabannin kasashen yammacin afrika dole zai samar da wata madogara dangane da dambarwar da take faruwa a kasar ta mali wacce ke yammacin nahiyar afrika.