An samu mutun daya da ya harbu da Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, watanni biyar bayan da aka sanar da kawo karshen cutar a kasar.
Ma’aikatar lafiyar kasar tace wani yaro mai shekara uku ne ya harbu da cutar ta ebola kuma ya mutu ranar 6 ga watan nan na Oktoba bayan an kwantar da shi a wani asibiti dake Beni, a lardin Kivu ta Arewacin kasar.
An aika da samfurin yaron zuwa Goma, babban birnin lardin, kuma an gano yana dauke da cutar mai saurin kisa.
Ma’aikatar tace yanzu haka suna aiki don ganowa da sanya ido kan kusan mutane 100 da yaron yayi mu’amala da su tare da feshin magani a cibiyoyin kiwon lafiya.
A wani labarin na daban hukumar lafiya ta Duniya WHO ta sanar da daukar tsauraran matakan yakar annobar cutar Ebola da aka samu ballarta a kasashen Guinea da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo, bayan aikewa da wata tawagar kwararru ta musamman zuwa kasashen biyu don tunkarar cutar.
Jami’an fiye da 100 da ake sa ran su kammala tattaruwa a Guinea zuwa nan da karshen wata, kari ne kan tawagar kwararru hukumar ta WHO 8 da suka bar babban Ofishin hukumar mai kula da nahiyar Afrka a birnin Braziville da za su jagoranci yaki da Ebolar a Guinea.
A ranar 14 ga watan nan ne Guinea ta sanar da samun bullar cutar ta Ebola karon farko tun 2016 lokacin da kasar ta yi fama da annobarta, gabanin nasarar shawo kanta a 2017.
Shugaban WHO shiyyar Afrika Dr Matshidiso Moeti ya ce matakan farko da za su dauka a yanzu shi ne bin diddigin wadanda suka yi mu’amala da masu cutar baya ga gwaji da bayar da magunguna da kuma fara yiwa jama’a rigakafi nan ba da jimawa ba.
A cewar Moeti yaki da cutar a wannan karon ka iya zuwa da tangarda la’akari da yadda Covid-19 ta kassara bangarorin lafiyar kasashe.
Tun a ranar 15 ga wata WHO ta girke tarin kayakin kulawar lafiya a Guinea inda za ta aike da alluran rigakafi dubu 11 a karshen makon nan gabanain wasu alluran dubu 8 da 500 da za a kai kasar daga Amurka.