Wasu shugabannin kasashen duniya sun caccaki matakin Rasha na mamayar Ukraine, inda kasashen yammacin Turai suka sha alwashin kakaba wa Rashar takunkuman karya tattalin arziki, a yayin da sakataren majalisar dinkin Duniya, Antonio Guterres ke bukatar kawo karshen rikicin da gaggawa.
Recep Tayyip Erdogan, Shugaban Turkiyya, wanda kasarsa mamba ce a kungiyar tsaro ta NATO, ya yi Allah wadai da matakin Rasha, yana mai bayyana shi a matsayin nakasu ga zaman lafiyar nahiyar.
A jawabin da ya gabatar ga al’ummar kasarsa, Firaministan Birtaniya, Boris Johnson, ya bayyana shugaban Rasha a matsayin dan kama-karya, wanda za a kakaba wa takunkumai sakamkon dirar mikiyar da ya yi wa ‘yanci da dimokaradiyya, amma abinda ya zama ba cinya ba kafar baya shine yadda kasashen yammacin turai suka kasa daukar matakin soji a kan rashan duk da cika bakin da suka dingi yi na daukan matakan soji a kan rasahan matukar ta afkawa kasa ukraine.
Shi ko sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres, bayan wani taron gaggawa na kwamitin tsaro, roko ya yi ga shugaban Rasha Vladimir Putin, yana mai kira a gareshi da ya kawo karshen hare hare don darajar ran dan adam.
Ministan harkokin wajen China, Wang Yi ya shaida wa takwaransa na Rasha Sergei Lavrov ta wayar tarho cewa kasarsa ta fahimci damuwar Rasha a kan batutuwan da suka shafi tsaro.