Duniya Na Kiran Bangarori A Iraqi Su Kai Zuciya Nesa.
Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa na kiran a kai zuciya nesa bayan kara tsunduma rikicin siyasa a Iraqi.
Amurka da faransa da Majalisar Dinkin Duniya duk sun yi irin wannan kiran tare da bayyana damuwa game da halin da ake ciki a Iraqin.
Babban sakataren MDD, Antonio Guteress, ya bukaci kai zuciya nesa tare da kiran dukkan bangarorin dasu dauki matakan da suka dace domin kwantar da hankali game da dambarwar da aka shiga.
Rahotanni daga Iraqin dai na cewa mutane 15 ne suka mutu lokacin da wani gungun masu dauke da makamai dake biyaya ga babban mai fada a ji nan a kasar Moqtada al-Sadr, suka bude wuta a yankin nan na Green Zone da birnin Bagadaza da ya kunshi manyan cibiyoyi na gwamnati da ofisohin jakadanci na kasashen waje.
Tuni dai aka kafa dokar hana fita tun daga yammacin jiya.
READ MORE : Makomar Libya Tun Bayan Shigar NATO A Cikin Lamurran Kasar.
Kasar ta kara tsunduma rikicin siyasa ne bayan da babban mai fada a jin Moqtada al-Sadr, ya sanar da janyewa gabadaya daga harkokin siyasa. A kasar.
READ MORE : Najeriya Na Ci Gaba Da Tafka Asarar Dayen Man Fetur Da Ake Sacewa.