Duk mayakan sa- kai daga Afirka da ke son taimaka wa Ukraine a yakin da ta ke da Rasha zai biya akalla dala dubu guda na visa da kuma tikitin jirgin gabanin samun damar iya kai dauki.
Babban sakatare a ofishin jakadancin na Ukraine Mr Bohdan Soltys ya tabbatar da cewa duk dan Najeriyar da ke son shiga yakin dole sai yana da horon Soji haka zalika sai ya biya dala dubu guda dai dai da kusan Nairar Najeriyar dubu 500.
Tuni dai wasu ‘yan Najeriyar suka fara janyewa daga yunkuri kai dauki kasar ta Ukraine a cewar Jaridar saboda yawan kudin da aka bukata kafin kai wannan gudunmawa.
Kashin farko na ‘yan Najeriya da suka makale a Ukraine dake yaki da Rasha ya isa filin tashi da saukara jiragen saman Abuja, babban birnin kasar da safiyar wannan Juma’a.
Shugabar ‘yan Najeriya mazauna ketare Abike Dabiri Erewa ta wallafa haka ta shifin twitta, tare da sanya hotunan isar ‘yan Najeriyar cikin jirgin saman Max Air samfurin VM602 a filin Namdi Azikwe dake Abuja.
Shima Shugaban kwamitin harkokin waje a Majalisar Wakilan Najeriya Yusuf Buba dake cikin jami’an gwamnatin kasar da suka je Bucharest, babban birnin Romania domin taho da ‘yan Naeriyar ya tabbatar da isowar dalibai 451 zuwa gida.