Dubban magoya bayan shugaban Tunisiya Kais Saied sun yi gangami a babban birnin kasar da wasu biranen a wannan Lahadi don nuna goyon baya ga dakatar da majalisar kasar da kuma yin alkawarin sauya tsarin siyasa, matakin da masu sukar shugaban ke kira juyin mulki.
A ranar 25 ga watan Yuli, bayan watanni na rashin jituwar siyasa, shugaba Saied ya kori Firanminista, kana ya dakatar da majalisar dokoki sannan ya karawa kansa karfin ikon.
A wani labarin mai kama da wannan shugaba Kais Saied na Tunisia ya sanar da nadin Najla Bouden matsayin Firaminista wadda za ta zamo mace ta farko a tarihin kasar da za ta hau wannan kujera dai dai lokacin da shugaban ke ci gaba da fuskantar boren al’umma.
Nadin na Najla Bouden na zuwa bayan da shugaba Kais ya rushe gwamnatin Hichem Machichi a ranar 25 ga watan Yuli baya ga dakatar da majalisar kasar tare da karawa kansa karfin iko wanda ya tunzura al’ummar kasar.
Tuni dai zanga-zanga ta zafafa a sassan kasar ta Tunisia don kalubalantar matakin shugaban na dakatar da kundin tsarin mulki tare da kwace iko da bangaren shari’a.
Sakon bidiyon da Ofishin na Kais Saied ya saki a Facebook ya nuno shugaban tare da Firaminista Bouden lokacin da ya ke bayyana mata bukatar ganin ta tabbatar da kafa gwamnatin nan da sa’o’I ko kuma kwanaki masu zuwa.
Shugaban a jawabinsa bayan nadin, y ace matakin da ya dauka girmamawa ce ga matan kasar dama daukacin al’ummar kasar wadda ke fatan samar da daidaito tsakanin al’umma.
Bouden za ta zama Firaministar Tunisia ta 10 tun bayan hambarar da gwamnatin Zine El Abedine Ben Ali yayin juyin-juya halin kasar a 2011.
Najla Bouden, mai shekaru 63 wadda masaniyar ilimin albarkatun karkashin kasa ce ta rike mukamin daraktar hukumar ilimin kasar gabanin zama mamba a hukumar kula da ilimi mai zurfi.