Dubban jama’a ne ke zanga-zanga a duk fadin kasar Faransa dan nuna adawarsu ga kisan da Isra’ila ke zirin Gaza.
A duk fadin kasar Faransa Dubban jama’a magoya bayan Falasdinu sun gudanar da tattaki domin yin Allah wadai da zalunci da laifukan yaki da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza.
Duniya ta yi mamakin abin da aka yi wa lakabi da “Kisan fulawa”; mutuwar Falasdinawa sama da 100 tare da jikkata wasu kusan 800 a lokacin da sojojin Isra’ila suka bude wuta kan fararen hula da ke jiran abinci.
Sama da mutane 600,000 a Gaza ko kuma kashi 25% na al’ummar kasar a halin yanzu suna cikin matsananciyar yunwa.
Duba nan:👇👇
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci gaskiya, adalci, da mutunta dokokin kasa da kasa tare da yin kira da a tsagaita bude wuta a zirin Gaza cikin gaggawa.
Shekaru hudu da suka gabata Macron ya tilastawa kudirin doka wanda ya kwatanta kyamar sahyoniya da kyamar bakar fata, duk da bambance-bambancen da ke tsakanin su biyun.
Masu zanga-zanga da dama ne dauke da hotunan marigayi sojan Amurka, Aaron Bushnell, wanda ya cinna wa kansa wuta a ofishin jakadancin Isra’ila da ke birnin Washington, bayan da ya bayyana cewa ba zai ci gaba da hada baki wajen aikata kisan kare dangi a Gaza ba.
A lokacin da Isra’ila ta fara mamaye Gaza, Faransa ta kafa dokar hana zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu a duk fadin kasar.
Duba nan:👇👇