Dubban Falasdinawa Sun yi Zanga-zangar Adawa Da Ziyarar Shugaban Amurka A Gabas Ta Tsakiya.
Rahoranni sun nuna cewa dubban falasdinwa ne suka fito kwansu da kwarkwatarsu a yankin gaza domin adawarsu da ziyara da shugaban kasar Amurka Joe biden ke yi a yankin, biden ya nuna cikakken goyon bayansa ga gwamnatin Isra’ila tun bayan da ya da hau kan madafun iko
A ranar laraba ce dai Biden ya isa birnin Tel Aviv inda ya fara rangadi na farko a irinsa tun bayan da ya kama aiki, kungiyar Hmas ta zargi Biden da fifita bukatun HKi akan hakkokin falasdinawa da aka danne musu da kuma batun tabbatar da tsaro a yankin
Haka zalika ita ma kungiyar Jihadil Islami ta zargi gwamnatin Amurka kan aniyarta na kara tsawaita mamaye isra’ila ke yi wa yankin da kuma zaluntar falasdinawa da take yi
READ MORE : Biden Ya Gargadi Bin Salman Game Da Sake Maimaita Wata Tabargaza Bayan Kisan Khashoggi.
Daga karshe sauran kungiyoyin falasdinu sun yi gargadi game da hadarin dake tattare da agenda Amurka na kara karfafa gwamnatin Isra’ila a yankin da kuma kara fadada yawan kasashen da za su kulla hulda da ita.
READ MORE : Masar Za Ta Janye Sojojinta Daga Cikin Tawagar MDD Dake Mali.