Duk da takunkumin da Isra’ila ta saka, dubban Falasdinawa daga yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye sun samu damar shiga Masallacin Ƙudus da ke Gabashin Birnin Ƙudus a ranar Juma’a ta farko ta watan Ramadan, don gabatar da sallarsu ta mako-mako a cikin jam’i yayin da suke azumi.
“Musuulmai kusan 80,000 ne suka yi Sallar Juma’a a Masallacin Ƙudus,” in ji Ma’aikatar Kula da Harkokin Musulunci a Birnin Ƙudus a cikin wata sanarwa.
Sheikh Ekrima Sabri, babban limamin Masallacin Ƙudus, ya yaba wa Falasdinawa muminai kan shiga masallacin duk da takunkuman Isra’ila.
“Kwarararku mai albarka tana isar da saƙo ga masu kwaɗayin shiga masallacin cewa ba ruwansa da rarrabuwar kawuna kuma na Musulmai ne kawai, babu inda za a yi sulhu ko a bar wani ɓangare nasa,” ya shaida wa masallatan.
Sabri ya bukaci al’ummar Musulmi da su zo Masallacin Ƙudus, yana mai cewa, “Idan aka hana su, za su iya yin salla a inda ta riske su, tare da fatan samun ladan yin salla a Masallacin Ƙudus.
Masar na neman a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza: Sisi
Shugaba Abdel Fattah el Sisi ya ce Masar na neman a tsagaita wuta a Gaza, da ƙara shigar da kayan agaji, da ba da damar ‘yan gudun hijira a kudancin yankin su koma arewacin kasar.
Masar na neman a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza: Sisi / Hoto: Reuters
Sisi, wanda ke magana a cikin wani saƙon faifan bidiyo, ya kuma yi gargadi game da haɗarin kutsen da Isra’ila ke da shi a garin Rafah da ke kan iyaka.
Hamas ta gabatar da shirin tsagaita a Gaza, ta mayar da hankali wurin musayar fursunoni
Ƙungiyar Hamas ta gabatar da shirin tsagaita wuta a Gaza ga masu shiga tsakani inda matakin farko zai haɗa da sakin matan Isra’ila da ƙananan yara da tsofaffi da marasa lafiya cikin waɗanda ta yi garkuwa da su, yayin da ita kuma za a sakar mata fursunoni Falasɗinawa 700 zuwa 1000, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana, yana mai ambato takardar da ƙungiyar ta tsara game da batun
Cikin waɗanda ƙungiyar take so a saka har da fursunoni Falasɗinawa guda 100 da Isra’ila ta yi wa ɗaurin rai-da-rai da kuma “mata da Isra’ila ta ɗauka aiki.”
Hamas ta ce za ta amince game da batun daina buɗe wuta na dindindin bayan an aiwatar da wannan shirin da ta gabatar, a cewar bayanan da ke cikin takardar.
Kazalika ta ce za a ƙulla yarjejeniya kan tsayar da ranar da Isra’ila za ta janye daga Gaza duka bayan wannan mataki na farko.
DUBA NAN: Tinubu Ya Bukaci A Kawo Karshen Matsalar Manoma Da Makiyaya
Ƙungiyar wacce ke gwagwarmayar kare hakkin Falasɗinawa ta ce za a saki mutanen da ake tsare da su na dukkan ɓangarorin biyu a mataki na biyu na yarjejeniyar da ta gabatar.