Duban Mutane Sun Fito Gangamin Bukatar Gyara A Dokokin Mallakar Bindigogi A Kasar Amurka.
Dubban mutane ne suka fito kan tituna a birane fiye da 450 a duk fadin Amurka don nuna rashin amincewarsu kan yadda kissan gamagari, ya yawaita a kasar, sannan suka bukaci majalisun dokokin kasar su yiwa wadannan dokoki garan bawul don samun zaman lafiya a kasat.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a cikin wannan shekara ta 2022 kadai an sami kissan gamagari har sau akalla 254 a duk fadin kasar wanda ya kai ga rasa rayuaksn mutanen da dama.
A birnin Washington D C babban birnin kasar Inda aka gudanar da taron mafi girma magajin garin birnin Muriel Bowser ta y i jawabi a taron in take cewa muna bukatar dokokinmallakar makamai wadanda hankali yake iya amincew ada su. Muriel ta ce kasashen duniya da dama ba sa mummunan rayuwar da muke yi a Amurka.
READ MORE : Ukrain; An Yake Wa Yan Burtaniya 2 Da Morocco Guda Hukuncin Kisa.
Matsalar mallakar bindiga dai ta zama babba a Amurka don kamfanonin kera makaman sun damu da riban da suke samu kawai, a yayinsa kasar take kara fadawa cikin kissan gama gari wanda ya hana mutane da dama zaman lafiya a kasar.