Shugaba Muhammadu Buhari ya roki takwararsa na Hadaddiyar Daular Larabawa UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan na a sassauta takunkumin da aka kakabawa yan Najeriya na hanasu shiga Dubai.
Yan Najeriya da dama na shiga birnin ta Dubai domin kasuwanci da yawon ganin Ido.
Shugaban yayi haka ne ta wani hira da sukayi ta hanyar tangaraho da shugaban kasar Dubai din, rahoton DailyTrust.
Tunda fari dai, Buhari ya kira Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan ne domin yayi masa jaje abisa mutuwar surukar sa, malama Maryam Al-Falasi, a yayin gudanar da wata tattaunawa mai muhimmanci tsakanin kasashen guda biyu.
A wani sako da mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya fitar, ya shaida cewa Shugaba Buhari ya bukaci takawaran nasa na daya kara duba hana bawa yan najeriya masu burin shiga kasar sa da yayi.
Ya tabbatar da cewa, sa-toka-sa-katsin da yake faruwa tsakanin ofisoshin kasashen nan guda biyu sakamakon halayyar daidaikun yan Najeriya marasa kishin kasa, an riga da tuni an warware su a jakadance, tare da kara tabbatar da cewa babu wata kasa da zata yadda da ayyukan bata gari ko wace iri ce.
To amma, shugaba buhari ya kara jaddada cewar, gwamnatin Najeriya da yake jagoranta a shirye take ta hukunta duk wani mai aikata laifuka a kasar Dubai ta hanyar bin matakan doka da aka tsara a shari’ance.
Sannan, shugaban ya kara da tabbatar da cewa, a kyale hukumomin da abin ya shafa dasu wararware shi a tsakanin kasashen guda biyu masu albarka.
Bayanin ya kara da cewa, tuni ma shugaba Buhari ya bada umarnin da kamfanin jigilar jiragen sama na Emirates da yaci gaba da hada hada a lunguna da sakuna na kasar nan.
Idan dai za’a iya tunawa, tun wajen 2022 ne dai kamfanin jigilar jiragen sama na Emirate ya tsaida ayyukan sa a ilahirin kasar nan sakamakon gaza biyan kudade da gwamnatin najeriya take binsa.
1: Majalisar Magabata Sai dai kuma shugaba Buhari ya tabbatarwa Shugaban Dubai cewa lamarin na kamfanin Emirate yana samun kulawa ta musamman daga gwamnatin najeriya, hada da sauran kamfanunnuka mallakin kasashen waje, domin tuni aka umarci babban bankin najeriya na CBN daya kara basu adadin kudaden kasar waje domin gudanar da ayyukan sub a tare da samun wani balahira ba ga kamfanin.
Source:LegitHausa