DRC; Mutum 75 Ne Suka Mutu Sanadiyyar Hatsarin Jirgin kasa.
A DR Congo adadin mutanen da suka mutu biyo bayan wani hatsarin jirgin kasa a yankin kudu maso gabashin kasar ya kai 75.
An kuam samu wasu mutum 125 da suka jikkata sanadiyyar gocewar jirgin kasa daga kan layin dogo da ya auku a ranar ALhamis da ta gabata.
READ MORE : Tsohon Shugaban America Ya Kamu Da Cutar corona.
Darakta janar na kamfanin kula da sufurin jiragen kasa na kasar, Fabien Mutomb, ya ce gocewar jirgin mai tarago 15, ta auku ne a gundumar Lubudi na lardin Lualaba dake kudu maso gabashin kasar.
A cewar ma’aikatar yada labarai ta kasar, jirgin ya rasa iko da taragonsa da dama, inda ya fada cikin wani kwazazzabo saboda lalacewar inji.