Dan takarar shugabancin Amurka na jam’iyyar Republican Donald Trump, ya bayyana goyon bayansa ga kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza, a cikin kalamai kaɗan da ya ta taɓa yi a fili kan fadan, yayin da kasashen duniya ke ci gaba da matsin lamba kan Amurka na ganin ta jawo hankalin ƙawayenta.
“E,” Trump ya amsa lokacin da aka tambaye shi yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Fox ko yana goyon bayan Isra’ila.
DUBA NAN: Babbar Alakar Da Najeriya Ta Kulla Da Qatar
Sai ɗan jaridar ya tambaye shi ko tsohon shugaban na goyon bayan yadda Isra’ila ke aiwatar da mamaya a Gaza.
“Ana buƙatar gamawa da matsalar,” in ji Donald Trump.
Amurka ta buƙaci MDD ta goyi bayan tsagaita wuta na wucin-gadi a Gaza don ƴantar da fursunoni
Amurka ta sake yin gyaran fuska a wani daftarin ƙudiri na Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya don goyon bayan “tsagaita wuta nan da nan na kusan makonni shida a Gaza tare da sakin dukkan waɗanda aka yi garkuwa da su,” a cewar bayanan da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani.
Layi na uku ta rahoton – wanda da farko Amurka ta gabatar makonni biyu da suka gabata – yanzu yana nuna kaifafan maganganun da Mataimakiyar Shugaban Ƙasa Kamala Harris ta yi.
Daftarin farko na Amurka ya nuna goyon baya na “tsagaita wuta ta wucin-gadi” a cikin kisan gillar da Isra’ila ta yi a yankin Falasɗinawa da ta yi wa ƙawanya.
Amurka na son duk wani goyon bayan kwamitin sulhu na tsagaita wuta ya kasance yana da alaƙa da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.
Amurka ta harbo makami mai linzami da jirage marasa matuƙa da ƙungiyar Houthi ta harba
Wani jirgin ruwa na Amurka ya harbo jirage marasa matuƙa da makami mai linzami da ƴan Houthi na Yemen suka harba a cikin Bahar Maliya, in ji jami’an Amurka, a daidai lokacin da sojojin ruwan Indiya suka fitar da hotunansu na yadda suka kashe gobarar da ta kama a cikin wani jirgin ruwan kwantena da ƴan Houthi suka fara kai wa hari.
Harin na Houthi ya haɗa da jirage marasa matuƙa masu ɗauke da bama-bamai da makami mai linzami guda ɗaya na kakkaɓo jiragen ruwa, in ji rundunar sojin Amurka.
Daga baya Amurka ta kai wani hari ta sama, inda ta lalata makami mai linzami guda uku da jiragen ruwa marasa matuƙa guda uku masu ɗauke da bama-bamai, in ji rundunar ta tsakiya.