An samu tsohon shugaban ƙasar Donald Trump da laifin aikata laifuka 34 da suka shafi karya bayanan kasuwanci, wanda ke zama laifi na farko da aka samu tsohon shugaban Amurka da shi. Zargin ya samo asali ne daga zargin cewa Trump ya ɓoye wani kuɗi da tsohon lauyansa ya bayar na rufe bakin tsohuwar fitacciyar jarumar fina-finai, Stormy Daniels jim kaɗan gabanin zaɓen 2016.
An shafe makonni shida ana shari’ar kuma an haɗa da shaidu 22 da suka haɗa da Daniels da kanta.
Donald Trump, wanda ya ƙi amsa duk wasu tuhume-tuhume da ake yi masa, kuma ya musanta aikata laifin yin lalata da Daniels, yanzu haka yana fuskantar shari’ar da aka shirya yi a ranar 11 ga watan Yuli.
Wannan hukunci mai cike da tarihi ya biyo bayan kwanaki biyu na shawarwarin alƙalai, kuma ya zo a muhimmin lokaci na siyasa, a tarihi babu wani shugaban Amurka da ya taɓa fuskantar shari’ar laifi a baya.
Ana sa ran ƙarin cikakkun bayanai za su fito yayin da ranar yanke hukunci ta ke gabato.
A wani labarin na daban ami’an tsaro a Jamhuriyar Nijar sun cafke daya daga cikin kasurguman ‘yan bindigar da suka addabin jama’a musamman a cikin Jihar Zamfara wanda aka fi sani da suna Baleri.
A ranar Talata ne runduna ta musamman da ake kira ‘’Farautar Bushiya” ta cafke Balari da wasu dimbin yaransa a garin Tankama da ke yankin Gidan Runji a Jihar Maradi daf da iyakar Nijeriya da Nijar.
Jami’an tsaron sun kai samame ne a Rugar Kowa Gwani bayan da suka samu bayanan sirri da ke cewa ‘yan bindigar dauke da makamai sun tattaru a wannan kauye.
Lokacin da yake gabatar da ‘yan bindigar a gaban mahukunta, babban kwamandan rundunar ta ‘’Farautar Bushiya’’ Kanar Mohamed Almoctar Niandou, ya ce za su ci gaba da jajircewa domin tabbatar da tsaro a kan iyakokin kasashen biyu.
Baleri, ya kasance daya daga miyagun ‘yan bindigar da suka addabin jama’a musamman a Jihar Zamfara, sannan daya daga cikin baraden da kasurgumin dan bindigar nan Bello Turji ke alfahari da su wajen kai hare-hare da kuma yin garkuwa da mutane musamman a yankin Arewa maso Yammaci.
DUBA NAN: Kotu Zata Cigaba Da Sauraron Karar Neman Hana Ganduje Bayyana Kansa A Shugaban Jam’iyyar APC
Kimanin wata daya da ya gabata, jami’an tsaron Jamhuriyar Nijar sun yi nasarar cafke wani dan bindigar mai suna Kachalla, tare da tasa keyarsa zuwa Yamai domin ya fuskanci shari’a.