Guterres na wadannan kalamai ne ga manema labarai, jim kadan bayan kammala taro kan wata gidauniya da aka kaddamar da nufin taimaka wa jama’ar Afghanistan.
A cewar sa sanya idanun kasashe duniya da kuma yin mu’amala da gwamnatin Taliban ne kadai zai ceto jama’ar kasar daga matsanacin talauci da yunwa da kuma kare su daga cin zarafin dan adam, saboda haka yin hakan na zaman dole kan kasashen duniya.
Taron da aka gudanar ranar Litinin, na da nufin samar da wata gidauniya da za’a tara akalla dala miliyan dari 6 don tallafa wa jama’ar Afghanistan da yanzu haka ke fuskatar matsanacin talauci da tsananin yunwa sakamakon tsayawar al’amurra cik, tun bayan da Taliban ta karbe iko da gwamnatin kasar.
Tun a tsakiyar watan Agusta lokacin da Taliban ta karbe iko da mulkin Afghanistan ne kasashe suka fara yanke hulda da Afghanistan da kuma cin alwashin kauracewa duk wata mu’amala da ita, abin da Guterres ke ganin cewa gurguwar shawara ce.
A ganin antonio guterres ke ganin bazai haifan da da mai ido ba, kuma indai an so a samu sassaucin lamurra dole ne kowacce kasa tayi mu’amala da taliban a matsayin ta na gwamnatin kasar afghanistan.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa Afghanistan na cikin hatsarin fukantar tabarbarewar al’amura, muddin kasashen duniya suka gaza daukar matakan samar da hanyoyin samun kudaden shiga ga kasar.
Sa’o’i bayan sake kwace iko da Taliban ta yi a Afghanistan karo na biyu, Amurka, da kasashen Turai da kuma manyan hukumomin Duniya suka katse baiwa kasar tallafi, da zummar dakile karfafa kungiyar ta Taliban.
A bayan bayan nan, Hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya UNDP ta fitar da wani rahoto da ya ce kimanin kashi 97 cikin 100 na al’ummar Afghanistan na iya fadawa cikin kangin talauci matukar ba a magance rikicin siyasa da tattalin arzikin kasar ba.
A halin yanzu kusan dala biliyan 10 na babban bankin Afghanistan da ke kasashen waje, hukumomin kasa da kasa suka kwace domin dakile kungiyar Taliban.
Sai dai wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Afghanistan Deborah Lyons ya shaida wa Kwamitin Tsaro a ranar Alhamis cewa ana bukatar samun hanyar shigar da kudi cikin kasar domin hana durkushewar tattalin arziki da tsarin zamantakewa lura da cewa kasar ta Afghanistan na fuskantar tarin matsaloli, ciki har da faduwar darajar kudin kasar, hauhawar farashin kayan abinci da man fetur da kuma karancin tsabar kudi a bankuna masu zaman kansu.