Sabon shugaban rundunar sojojin Burtaniya ya yi imanin cewa dole ne sojin Kasar su kasance a shirye don ‘yaki kuma da nasara’, yayin da yake tsokaci kan yakin da ake ciki a Turai Tsakanin Rasha da Ukraine.
Da yake magana kan wani hari da Rasha takai a Ukraine, Janar Sir Patrick Sanders, babban hafsan hafsoshin sojojin Kasar, ya yi gargadin cewa dole ne sojojinsa su kasance cikin shirin tunkarar yaki da zaluncin shugaban Rasha, Vladimir Putin.
Ya kara da cewa, dole ne sojojin Burtaniya su zama cikin shiri, da zarar kungiyar NATO tayi kira su amsa kira don Yaki a gabashin Kasashen NATO.
Da ma dai tuni ya ankarar da rundunarsa Maza da Mata da dole su sake yin shiri don yin yaki a tarayyar Turai.
Akalla fararen hula 28 ne suka mutu a hare-haren Rasha a ranar Litinin, a wani harin makami mai linzami da aka kai kan wata cibiyar hada-hadar jama’a.
A wani labarin na daban Kotu a Senegal ta yanke hukuncin daurin talala na watanni 6 a kan wani dan majalisar dokokin kasar mai suna Dethie Fall saboda samun shi da laifin tsara tarzomar da aka yi ranar 17 ga wannan wata don nuna rashin amincewa da matakin kotu, wadda ta hana ‘yan adawa tsayawa takara a zaben ‘yan majalisar da za a yi a bana, yayin da ta sallami wani dan majalisar wato Mame Diarra saboda rashin gabatar da shaidar da ke tabbatar da cewa ya aikata laifi.
Tun farko kimanin mutane 84 ne suka gurfana gaban kotun a jiya litinin ciki har da ‘yan majalisun 2 daga jam’iyyar adawa kan zargin watsi da umarnin kotu da ta haramta zanga-zangar kalubalantar matakin hana ‘yan adawa tsayawa takara a zabe mai zuwa.
Mahukuntan Senegal sun haramta zanga-zangar ta ranar 17 ga watan Yuni ne saboda fargabar yiwuwar fuskantar tashe-tashen hankula a wasu sassan kasar sakamakon fusatar da jama’a suka yi da matakin ‘yan adawa shiga zaben ‘yan Majalisa.
Sai dai duk da wannan mataki sai da rikici ya barke a Dakar da yankin Casamance da ke kudancin Seengal saboda yadda matasa suka bijirewa umarnin na Kotu kan zanga-zangar, inda bayanai suka ce mutane 3 sun mutu yayinda wasu 200 suka jikkata.