Majalisar dokokin kasar Denmark ta amince da wata doka a yau Alhamis, inda ta haramta tozarta litattafai masu tsarki da suka hada da kur’ani mai tsarki.
A rahoton Arabi 21, majalisar dokokin Denmak ta zartar da wata doka a yau Alhamis, bisa ga abin da ta haramta “dabi’un da ba su dace ba” tare da littattafai masu tsarki da nassosi tare da hana kona kur’ani sosai.
A watannin baya-bayan nan ana ci gaba da tozarta kur’ani mai tsarki da wuraren ibada na Musulunci a kasar Denmark da wasu kasashen Turai, lamarin da ya harzuka musulmi da kasashen musulmi.
Majalisar dokokin Denmak mai wakilai 179 ta amince da kudirin dokar da ta haramta “halayen da ba su dace ba tare da rubuce-rubuce masu muhimmanci ga al’ummomin addini” tare da kuri’u 94 da suka amince da kuri’u 77 na adawa.
Ministan shari’a na Denmark Jitter Humelgaard ya ce a watan Agustan da ya gabata: “Kona kur’ani na baya-bayan nan yana da tasiri kan barazanar da ake fuskanta a yanzu. “Muna cikin wani yanayi mai hatsari kuma muna bukatar tsauraran matakan kula da iyakokin Denmark don tunkarar barazanar da Denmark ke fuskanta.”
Kasashen Sweden da Denmark da Holland sun fuskanci laifukan cin zarafin kur’ani mai tsarki a cikin shekaru daya ko biyu da suka gabata daga wasu masu tsattsauran ra’ayi wadanda suka saba aikata wannan laifi a gaban ofisoshin jakadancin kasashen musulmi. daga cikin kasashen turai da aka ambata an kirasu zuwa kasashen musulmi, a daya bangaren kuma wasu kasashen musulmi sun kira jami’an diflomasiyyarsu daga wadannan kasashen turai.
Kazalika hukumomin kasar Sweden na nazarin hanyoyin da za a bi wajen magance wulakanta kur’ani mai tsarki.
Source: IQNAHAUSA