Ya ce tun a shekarun baya ne ‘yan ta’adda da suka addabe su a kauyensu, hakan yasa ala tilas suka yi gudun hijira suka kaurace ma kauyen.
Muhammad ya ce,a lokacin gudun hijirar ne ya samu matsalar gani sakamakon irin makaman da ‘yan ta’adda suka rika harbawa a kan jama’a musamamn wadanda basu goyon bayansu.
Sakamakon haka ne kuma ya rika amfani da rikoda mai amfani da kaset wajen sauraren karatun kur’ani, kuma a cikin wadanann shekaru kasa da biyar ne ya hardace kur’ani mai tsarki baki daya.
Wannan dattijo dai ana bayyana shi da cewa yana da kaifin basira wajen rike komai a kwakwalwarsa, inda ya hardace suanayen dukaknin shugabannin kasashen duniya, da kuma sunayen manyan tekuna na duniya.
A wani labarin na daban kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a yau Asabar daruruwan mutane sun taru a kusa da tashar jiragen ruwa ta birnin Beirut, domin nuna farin cikinsu da shirin Iran na aike wa da katafaren jirgin ruwa da yake dauke da makamashi zuwa kasar ta Lebanon.
Rahoton ya ce wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jirgin na Iran wanda yake dauke da makamashi yake kan hanyarsa ta isa gabar ruwan Beirut, bayan da ya yada zango a gabar ruwan kasar Syria.
Kasar Lebanon dai ta shiga cikin matsanancin hali sakamakon rashin makamshi, bayan da Amurka da wasu kasashen turai suka dauki matakin takurawa kasar, da nufin ganin sun raunana kungiyar Hizbullah, wadda suke kallonta a matsayin babbar barazana ga gwamnatin yahudawan Isra’ila.