Wani mai nazarin lamurra a gabas ta tsakiya mai suna Mardkoi Kidor a wata makala yayi ikirarin cewa, dalilan takwas suka sanya Iran da Saudiyya suka kusanci juna tare da shiga tsakanin Chana, kuma yana da yakinin cewa farfado da alakar Iran da Saudiyya yana da tasiri mara amfani ga Tel-Aviv.
Sa’annan masu fada ajin Isra’ila suna cike da mamaki dangane da yarjejeniyar da ta faru tsakanin Iran da Saudiyyan kuma wannan ne babban razanin gwamnatin Isra’ila, hatta hadewar Bahrain da Hadaddiyar daular larabawa bisa wannan yarjejeniya ne.
Isra’iliyawa sun samu yakinin cewa tsakanin tashe tashen hankula dake faruwa a Isra’ilan da kuma yarjejeniyar farfado da alaka tsakanin Iran da Saudiyya yana da alaka ta kurkusa.
Jaridar Mustshriq ta Isra’ila ta tabbatar da cewa farkon wannan lamari farkawar Musulunci a karshen shekarar 2010 ne kuma ta rubuta cewa: «Saudiyawa sun fahimci cewa gwamnatin Amurka ta ture su gefe kuma tana kokarin ta kusanci makiyan su irin su Iran da Saudiyya»
A bisa ikirarin wannan mai sharhin lamurran na Isra’ila abu na biyu cikin dalilan shine sa hannu kan yarjejeniyar nukiliya wacce akayi da Iran din a shekarar 2015 tattare da cewa Saudiyya ta matukar nuna adawar ta da hakan.
Abu na uku guguwar kafafen yada labarai ne da kashe Jamal Kashshogi wani dan jaridar Saudiyya a shekarar 2018 a Istanbul, wannan ya matukar taba darajar Bin Salman a duniyar siyasar duniya wanda yanzu yake kokarin kankaro darajar sa ta hanyar shiryawa da Iran.