Daliban Jami’ar Lagos dake Najeriya sun gudanar da zanga zangar lumana domin nuna bacin ransu da kasa warware rikicin dake gudana tsakanin malamansu a karkashin kungiyar ASUU, da gwamnatin tarayya, abin da ya haifar da yajin aikin watanni 3.
Daya daga cikin shugabannin daliban Yinka Alabi ya bayyana wa RFI Hausa cewar alhakin yajin ya rataya ne a wuyar gwamnatin tarayya wadda ta mallaki jami’o’in saboda haka ya dace ta dauki duk matakan da suka dace wajen sasantawa da malaman.
Alabi ya ce sun gaji da zaman gida, kuma akasarin su shekaru na dada kama su, yayin da suke daukar shekaru 5 zuwa 6 kafin kammala karatun shekaru 4 saboda yaje yajen aikin.
Segun Adeyemi ya ce abin takaici ne kasar dake ikrarin neman ci gaba irin Najeriya na wasa da harkar ilimi wanda shine ginshikin ci gaban da ake samu a kowacce kasa.
Elizabeth Obinna wadda ta ce yajin aiki ya lalata karatun jami’a a Najeriya, ta zargi ‘yan Siyasar Najeriya gazawa wajen kare martabar ilimin yaran talakawa saboda ‘yayan su ba sa karatu a jami’oin, inda ta bukaci yin dokokin da za su tilasta wa jami’an gwamnati sanya ‘yayan su a irin wadannan jami’oi domin ba su kwarin gwuiwar kare martabar jami’oin a ko da yaushe.
Ita dai kungiyar malaman jami’o’in ta sanar da kara wa’adin ci gaba da yajin aikin har zuwa lokacin da gwamnati zata aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla.