A jiya Litinin ne manyan kasashen duniya da shuwagabannin kasashen Afrika suka gana a birni Rotterdam don duba irin hanyoyin da za’a bi wajen shawo kan matsalar dumamar yanayi rikice-rikice da ake fama das u a kasahen Afrika.
Manyan kasashen masu karfin tattalin arziki sun sha alwashin yin amfani da kudade da yawansu ya kai dala biliyan 25 nan da shekara ta 2025 don kara fadada kokarin da ake yi wajen shawo kan matsalar dumamar yanayi dake haddasa amabliyar ruwa fari da tsananin zafi a nahiyar
Rabin kudin bankin bunkasa nahiyar Afrika ne da hadin guiwar wakilai daga kasashen Denmark da birtaniya , faransa da kuma netherland suka yi alkawarin bayarwa, haka shi ma Asusun bada lamuni na kasa da kasa da sauran hukumomi sun bada goyon baya wajen kirkiro da wannan shirin.
Nahiyar Afrika na fatan yin amfani da kudaden wajen shawo kan matsalolin da canjin yanayi ke haifarwa kamar fari, ambaliyar ruwa , da kuma kara yawan shuka itatuwa da sauran abubuwan da za su bada kariya da kuma fadada karfin da suke das hi na samar da makamashi da ake sabuntawa.
A wani labarin na daban sabuwar firaministar Burtaniya Liz Truss ta kama aiki a hukumance kwana daya bayan zabenta a matsayin shugabar jam’iyyar Conservative.
Tsohuwar ministar harkokin wajen ta Biritaniya, ta gana da Sarauniyar Ingila a fadarta da ke Balmoral Castle da ke Scotland yau Talata a wani bangare na shirye-shiryen rantsar da ita a matsayin firaministar kasar ta gaba.
Wannan na zuwa ne bayan da a safiyar yau din firaminstan mai barin gado Boris Johnson ya gana da Sarauniyar in da ya mika takardar murabus dinsa.
Manyan kalubalen dake gaban sabuwar firaminsitar sun hada da na tattalin arziki a daidai lokacin da matsalar hauhawan farashin kayaki ke dada karuwa a Burtaniya.
Karin dai na da nasaba ne da karuwar farashin makamashi irinsu iskar gas da kuma wutar lantarki dake addabar kasashen turai da dama sakamakon rikicinsu da Rasha kan yakin Ukraine.
Source: ABNAHAUSA