Bayan da majalisar wakilan kasar Amurka ta zartas da kudurin doka game da aikin kayyade basussuka da kasar za ta iya karba, kafofin watsa labaru na kasashe daban daban sun bayyana a jiya Alhamis cewa, batun nan tamkar “dakatar da yaki na wucin gadi ne, wanda ba a kawo karshensa ba tukuna”.
Kudurin ya dakatar da lokacin fara yin amfani na dokar kayyade yawan bashin da gwamnatin kasar Amurka za ta iya ci har zuwa farkon shekarar 2025, haka kuma an kayyade kudaden da za a kashe a cikin kasafin kudi na shekarar 2024 da ta 2025.
Ga alama batun nan ya kau da damuwar wasu mutane.
Sai dai ko da majalisar dattawa ta kasar Amurka ta amince da kudurin a nan gaba, kuma shugaban kasar shi ma ya sanya masa hannu, shin da gaske ne za a iya warware matsalar ta wannan dabara?
Shin da gaske ne Amurka din da sauran sassan duniya suna cikin wani yanayi mai tsaro yanzu?
A halin yanzu, a kasuwannin takardun bashi na kasa da kasa an fi samun takardun shaidar bashin da ake bin gwamnatin kasar Amurka.
Saboda haka idan gwamantin kasar Amurka ta kasa biyan bashin, to, ita kasar da sauran kasashe daban daban za su shiga cikin mawuyacin hali.
Don tinkarar wannan yanayin da za a iya samu, kasar Amurka ta dauki wannan dabara: wato a dakatar da lokacin fara aiki na dokar kayyade bashin da za ta iya karba da tsawon shekaru biyu. Ko da yake wannan dabara ta dakatar da matsala kawai, maimakon warware ta daga tushe. Ban da haka kuma za ta sanya bashin da kasar Amurka ta ci dinga karuwa.
A matsayinta na kasa mafi tasirin tattalin arziki a duniya, muhimman alkaluman ma’aunin tattalin arzikin kasar Amurka na ci gaba da raguwa, kana ana fuskantar babban hadarin samun koma bayan tattalin arzikin kasar, yayin da dimbin bankunan kasar ke fuskantar mawuyacin hali, lamarin da ya haifar da wani yanayi na rashin tabbas ga sauran sassan duniya.
Yanzu, rikicin bashi na Amurka, wanda aka kwashe watanni da dama ana tinkararsa, yana ci gaba da haifar da matsaloli a kasuwannin kasa da kasa.
Daga cikin wannan “wasan matsorata” da jam’iyyun siyasan kasar Amurka suke yi, wanda ba a san lokacin da za a kawo karshensa daga tushe ba, wani ilimin da mutanen duniya suka samu shi ne, kasar Amurka ce ke haifar da babban hadari ga tattalin arzikin duniya.(Safiyah Ma)