Dakarun Sojojin Kasa Na Iran Za Su Fara Atisayen Soji Na Tauna Tsakkuwa Don Aya Taji Tsoro.
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojojin kasa na kasar iran za su fara wani Atisayen soji na kwanaki biyu mai suna Eqtidar don auna irin karfin da suke dashi da don tunkarar sabbin barazana da suke fuskanta.
Kakakin bataliayr dake jagorantar Atisayen na Eqtidar Birgediya janar Amir Cheshak ya fadi cewa za’a fara shi ne a yau laraba a barin Nasr Abda dake tsakiyar kasar iran , kuma zai samu halartar bangarorin soji daban daban na kasar kuma za’a ayi amfani da jirage marasa matuki sabbin makaman kariya.
Haka zalika ya kara da cewa damarun soji na musamman na kasar za su baje kolin sabbin dabarin yaki da suka kara kwarewa akai wajen kare kasa daga duk wata barazana daga makiya.
READ MORE : Liz Truss Ta Zama Sabuwar Firaministar Biritaniya.
Wannan atisayen yana zuwa ne yan kwanaki bayan da maikatar tsaron Iran ta bayyana cewa ta sanya sabbin naurorin tsaro na farar hula a manyen birane 51 a fadin kasar, domin sa ido da dakile duk wata barazana da ka iya fuskanta a cikin kankanin lokaci Isra’ila.
READ MORE : Rasha Ta Ce Ba Za Ta Sake Bude Bututun Iskar Gas Ga Kasashen Turai Ba.