Dakarun hadakar kasashen kudancin Afrika sun yi nasarar fatattakar mayakan da ke ikirarin jihadi a yankin Cabo Delgado da ke arewaci zuwa wajen kasar sai dai rundunar tsaro ta SADC ta ce sojin za su ci gaba da zama a yankin don kalubalantar duk wata barazana da ka iya kunno kai a kasar ta Mozambique.
Shugaban rundunar Mpho Molomo ya ce barazanar tsaro da hare-haren ta’addanci har yanzu na matsayin babbar matsalar Mozambique.
A watan jiya ne rundunar ta SADC ta tsawaita wa’adin dakarunta da kwanaki 90, sai dai a yanzu Molomo ya ce babu rana janye dakarun daga yankin duk da nasarar da suka samu ta fattakar ‘yan ta’addan.
Tun a watan Yulin da ya gabata ne, rundunar hadakar dakarun kasashen kudancin Afrikan 16 suka fara aikin yaki da matsalar tsaron da ta dabaibaye kasar ta Mozambique inda Rwanda a bangare guda ta aikewa kasar dakaru dubu guda.
Wasu rahotanni sun ce mayakan ta’addan yanzu haka sun fantsama wasu yankuna na Tanzania ciki har da Niassa da Nampula.
Tsawon shekaru 4 yankin na Cabo Delgado mai arzikin iskar gas ya shafe yana fama da matsalar hare-haren ta’addanci daga kungiyoyi masu ikirarin jihadi, wanda ya hallaka mutane fiye da dubu 3 da 340 baya raba wasu fiye da dubu 800 da muhallansu.
Karamar kungiyar ta’addancin wadda ta kira kanta da Al-Shabab bayanai sun ce basu da wata alaka kungiyar da ke Somalia mai makamancin sunan ko da yak e dukkaninsu na ikirarin tabbatar da mulki kan doron tsarin Islama.