Dakarun Sojoji 6 da mayaka masu ikirarin jihadi akalla 22 ne suka mutu, yayin fadan da aka gwabza tsakanin sojojin Najeriya da na Nijar da kuma ‘yan ta’addan gefe guda, a Yankin Tafkin Chadi.
Rundunar ta MNJTF ta kara da cewar dakarun ta da suka kwanta dama yayin fafatawar ta baya bayan nan sun hada da sojojin Najeriya 4 da na Nijar 2, yayin da wasu 23 suka jikkata, a lokacin farmakin da suka kawo karshensa a ranar Talatar da ta gabata.
Tarihi dai ya nuna cewar tun shekarar 1994 aka kafa ginshikin farko na rundunar hadin gwiwa ta MNJTF, inda a waccan lokacin ta kunshi sojojin Najeriya kawai, wadanda aka dorawa alhakin murkushe barazanar tsaro ta barayin shanu akan iyakokin kasar daga bangaren arewacinta.
A wani labarin na daban Hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ta fitar da wata sanarwa da ke gargadin cewar za a iya kai hare-haren ta’addanci a Abuja babban birnin kasar, a tsakanin ranakun 17 zuwa 31 ga watan Disamban nan.
Kwamanda Okoto ya ce ‘yan ta’addan, sun shirya shiga Najeriya ne daga Mali ta hanyar bi ta cikin Jamhuriyar Nijar.
Wadanda ake zargi da shirya kai hare-haren ta’addancin a Abuja dai sun hada da Drahmane Ould Ali, wanda aka fi sani da Mohammed Ould Sidat dan kasar Aljeriya, tare da wani mai suna Zahid Aminon dan kasar Nijar.
Sanarwar ta kuma ce tuni mutanen biyu da ake zargi suka samu mataimaka akalla 4 ‘yan Najeriya, abinda ya sanya tuni hukumomin tsaro suka kara kintsawa cikin shirin ko ta kwana.
Gargadin hukumar shige da ficen Najeriya ya zo ne makwani kalilan bayan da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta yi gargadin cewa, ‘yan ta’adda na shirin kai hare-hare kan sansanonin sojin da ke garuruwan kan iyakoki.
Tuni dai hukumomin tsaron Najeriya suka nemi ‘yan kasar da su kwantar da hankulansu, kasancewar a shirye suke wajen dakile duk wata barazana.