Dakarun sojin Ukraine ta ce sojojin kundunbalar Rasha sun sauka a Kharkhiv, birni na biyu mafi girma a kasar yau laraba, yayin da ake ci gaba da musayar wuta a garin.
Hukumomin kasar sun ce wani harin sama da dakarun sojojin Rasha suka kai wani ginin dake dauke da gidaje, yayi sanadiyar mutuwar fararen hula, abinda ya sa shugaba Volodymyr Zelensky ke zargin Rasha da aikata laifuffukan yaki.
Zelensky ya bukaci kasashen duniya da su taimakawa kasar wajen kawo karshen hare haren da Rasha ke kaiwa a Kharkiv wanda ya bayyana shi a matsayin laifuffukan yaki.
Kotun hukunta manyan laifuffuka dake Haque ta sanya ranakun 7 da 8 na wannan wata a matsayin ranakun da zata saurari zargin aikata laifuffukan yakin da ake zargin Rasha a Ukraine.
Kotun ta ce sauraren ba’asin ya biyo bayan bayanan da Ukraine ta gabatar mata wanda ya hada da kasha fararen hula da kuma tilastawa mutane kusan miliyan guda barin gidajen su, yayin da Majalisar Dinkin Duniya tace akalla mutane miliyan 4 zasu taimako sakamakon yakin, yayin da adadin na iy akaiwa miliyan 12 na da watanni masu zuwa.
A wani labarin na daban kuma Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana takwaransa na Rasha Vladimir Putin a matsayin shugaban kama karya wanda ke fama ta takunkumin karya tattalin arziki da kuma kadaici, sakamakon yadda kasashen duniya suka kauracewa kasar sa inda yake cewa duniya na yaki ne tsakanin mulkin dimokiradiya da kuma kama karya.
Shugaban ya ce ma’aikatar shari‘ar Amurka na kafa wani kwamitin ko ta kwana na musamman wadda za ta bincike laifuffukan da shugabannin Rasha ke aikatawa domin daukar matakai a kan kasar.
Biden ya ce suna hada kai da kawayensu na kasashen Turai domin kwace kasaitattun gidaje da lambunan da attajiran Rasha suka mallaka tare da jiragen sama na kansu wadanda suke shawagi da su zuwa kasashen duniya.
Shugaban wanda ya dauki dogon lokaci a jawabin nasa na sa’a guda yana tsokaci akan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, ya ce suna daukar matakai da dama a kan kasar inda ya ce, “kuma a daren yau ina shaidawa jama’ar kasar mu cewar na bi sahun kawayenmu na duniya wajen rufe sararin samaniyar Amurka ga daukacin jiragen saman Rasha”.
‘Yan majalisun Amurka sun yi ta tashi suna yi wa Biden tafi lokacin da yake gabatar da jawabin a zauren majalisar dokoki.