Dakarun Kawance Da Saudiya Ke Jagoranta A Yamen Suna Abin da Kungiyar ISIS Ta yi A Iraqi Da Siriya.
Jakadan kasar Yamen a birnin tahran Ibrahim Dailami ya fadi cewa laifukan yaki da kungiyar ISIS ta yi a kasashen Siriya da Iraqi shi ne abin da dakarun kawance da kasar saudiya ke jagoranta ke yi akan Alummar yamen,da taimakon hadaddiyar daular larabawa.
Ya kara da cewa kasar saudiya ta kafa rundunar soji daga kasashen larabawa daban –daban tare da taimako da dabarun yaki na kasar Amurka da Isra’ila wajen kai hare-hare ta sama da kasa da ruwa kan fararen hula a kasar yamen a shekara ta 2015 da nufin tabbatar da tsohon shugaban kasar Abdurabbu Mansur hadi kan madafun iko.
Daga karshe ya nuna cewa dakarun kasar ta yamen sun samu nasarori sosai wajen mayar da martani da kare kai daga hare-haren da saudiya ke kaiwa a lardin Ma’arib da Bayda da shabwa.
A tsawon shekaru 7 da kasar saduiya ta kaddamar da yaki kan kasar yamen ta rusta dukkan muhimman gine-ginen kasa da suka hada da cibiyoyin magani da ilimi da ababen more rayuwa.