Dakarun sojin Mali ta ce ta kashe mayaka 203 a wani samame da ta kai a wasu yankunan kasar, lamarin da ke nuni da karuwar ba ta kashi tsakanin dakarun gwamnati da kungiyoyi masu ikirarin jihadi a kasar da yaki ya daidaita.
A cewar wata sanarwa daga rundunar sojin ta Mali, dakarun gwamnati sun kashe mayaka 203, suka kuma kama 51, tare da kwace dimbim makamai.
Sanarwar na zuwa ne bayan rahotannin da suka karade kafafen sadarwar zamani a wannan makon cewa an kashe gwamman mutane, ciki har da fararen hula a yankin Moura.
Sai dai kamfanin dillancin labaran Faransa ta ce har yanzu ba ta kai ga tantance sahihancin rahotannin biyu ba.
‘Yan bindiga sun kashe akalla mutane 17 a wasu hare hare da suka kai kauyuka 4 a karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya, inda suka kuma yi awon gaba da dimbim dabbobi bayan sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi.
Wata majiya ta ce tun da tsakar ranar Alhamis ne ‘yan bindigar suka fara afka wa mutane, har ma suka shiga kasuwar Rafin Gero da ke ci, suka yi awon gaba da dimbin shanu da rakuma da sauran dabbobi.
Mazuna yankin sun ce duk da cewa mutane sun ruga cikin daji don neman tsira, ‘yan bindigar sun yi ta bin su a kan babura suna harbewa.
Ya zuwa lokacin hada wannan labari, babu wani karin bayani daga rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, kuma duk kokarin samun kakainta ya ci tura.