Dakarun Kare Juyin Musulunci Na Iran Sun Yi Tir Da Keta Hurumin Masallacin Qudus Da “ Yan Sahayoniya Suke Yi.
A wata sanarwa da dakarun kare juyin musuluncin na Iran su ka fitar a jiya Juma’a, sun yi tir da keta hurumin masallacin Quds da ‘yan sahayoniyar suke yi wanda laifi ne mai girma.
Har ila yau sanarwar ta ce; Abinda ‘yan sahayoniyar suke yi, zai kunna wutar sabon boren “Intifada” ne da zai zamarwa ‘yan sahayoniyar alakakai da masu goyon bayansu a cikin wannan yankin.
A jiya juma’a da asuba ne dai ‘yan sandan HKI su ka kutsa cikin farfajiyar masallacin Quds, tare da jefa hayaki mai sa hawaye da kuma kama Palasdinawa 400.
READ MORE : Macon Ya Samu Goyon Bayan Wasu Fitattun Mawaka Da ‘Yan Fim.
Wani sashe na sanarwar Dakarun kare juyin musulunci na Iran din; ( IRGC ) ya kunshi cewa;Abinda ‘yan sahayoniyar suka yi na keta hurumin masallacin Quds kuma a cikin watan azumin Ramadan mai alfarma, tare da jikkata fararen hula 150,ba zai haifar musu da, mai ido ba.
READ MORE : Burkina Faso Zata Dauki Sabbin Sojoji Dubu 3 Don Yaki Da Ta’addanci.
READ MORE : Amurka Da Najeriya Sun Amince Da Cinikin Jiragen Yaki Masu Saukar Angula 12.