Dakarun Kare Juyin Musulunci Na Iran Sun Yi Alwashin Daukar Fansa Kan Isra’ila.
Rahotanni sun bayyana cewa Dakarun kare juyin musulunci na iran sun sha Alwashin daukar fansa kari da makami mai linzami da sojojin Isra’ila suka kai a wajen birnin Damaskas na kasar siriya da yayi sanadiyar shahadar wasu masu bada shawar guda biyu na dakarun na IRGC
A acikin bayanan da hekdwatar ta IRGC din ta fitar ta nuna cewa gwamnatin Isra’ila za ta biya farashin abin da ta aikata. Kanar Ehsan Karbala’ poor da kuma kanar Mortana Saeed Nezhad su ne wadanda suka yi shahada sakamakon harin na Isra’ila a jiya litinin a wajen birnin damaskas fadar mulkin kasar Siriya.
Kasar iran ta ci gaba da kiyaye tsarin masu bada shawara a kasashen larabawa , domin taimaka musu wajen yaki da ta’adanci da suke yi, wanda a shekara ta 2017 tawagar masu bada shawarar sun taimakawa gwamnatin Siriya wajen yin galaba kan kungiyar ta’adda ta ISIS da kuma Daesha a kasar
Harin na jiya ba shi ne na farko da isra’ia take kaiwa kan iraniyawa masu bada shawara ba, ko a baya ma sojojin Isra’ila sun kai hari a sansanin T-4 dake kusa da garin Homa dake yamacin kasar Siriya a shekata ta 2018 kuma yayi sanadiyar shahdar da ma daga cikin Iraniyawa masu bada shawara .
Isra’ila tana goyon bayan kungiyoyin yan ta’adda a siriya dake adawa da gwamnatin Bashar Asad tun bayan mamayar soji da Amurka ta yi wa kasar siriya a shekara ta 2011