Dakarun kasar Faransa dake aiki a Menaka ta kasar Mali don yakar ‘yan ta’adda yau sun fice daga garin inda suka mikawa sojojin Mali sansanin su dake arewa maso gabashin kasar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke gargdain cewar ficewar sojojin Farnasar daga Menaka na iya jefa yankin cikin hadarin sake fadawa hannun ‘yan ta’adda.
Kakakin dakarun sojin Faransa Janar Pascal Ianni ya ce an kammala janyewar sojojin nasu daga sansanin cikin kwanciyar hankali, ba tare da samun wata matsala ba.
Janar Ianni ya ce ficewar dakarun na zuwa ne kafin kammala janyewar sojojin Faransa daga kasar kamar Mali baki daya kamar yadda aka tsara a bazarar bana, wanda zai kunshi mika sansanin sojin dake Gao hannun sojojin kasar da kuma kawo karshen aikin rundunar Barkhane.
Sai dai wakilin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Mali El-Ghassim Wane ya bayyana fargabar cewar janyewar dakarun zai haifar da matsala sosai ga Menaka.
Wane ya ce ya ziyarci garin makwannin da suka gabata, kuma mutanen cikin sa sun bayyana cewar ana iya kai musu hari a koda yaushe a garin dake dauke da baki ‘yan gudun hijira sama da 5,000.
Jami’in yace muddin aka samu haka, babu wani wuri da fararen hular zasu samu mafakar da ta wuce sansanin sojin Majalisar Dinkin Duniya.
Wane yace ganin yadda ake da sojojin Mali da basu da yawa a yankin da kuma dakarun samar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya 600 kare fararen hula da kuma jami’an majalisar da kuma kadarorin su zai yi targade wajen kai dauki ga wadanda za’a kaiwa hari.
Yayin taron Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya Jakadan Faransa Nicolas de Riviera yace zasu ci gaba da taimakawa sojojin kasar Mali da dakarun Majalisar ta hanyar sojojin sama, amma kuma Ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop yace basa bukatar wani taimako na sojin Barkhane wajen kai harin sama a cikin kasarsu.